Zumunci Mai Dadi
funny
A rayuwa, ka yi hakuri da wasu, ka nuna tausayi ga kowa, domin kowanne rai na ɗauke da labari da ba a sani ba. Ka zama haske a cikin duhu na wani.
A rayuwa, ka yi hakuri da wasu, ka nuna tausayi ga kowa, domin kowanne rai na ɗauke da labari da ba a sani ba. Ka zama haske a cikin duhu na wani.
ZUMUNCI MAI DADI NA YIWA Kowa Fatan Alkairi
Ya Allah
Ka Kawomana Zaman Lafiya ka Karemana Musulman Duniya Baki Daya Alfarmar Annabi Muhammad S.A.W.
26/06/2023
Falalar Azumin Ar-fah
Azumin ar-fah shine azumtar ranar tara g watan zulhajj ga wanda bai samu damar zuwa ai'kin hajji ba domin neman kusanci ga Allah subhanahu wata'ala tare da raya sunnar Annabi Muhammad Sallallahu Alaihi Wasallam.
Annabi Muhammad Sallallahu Alaihi Wasallam yana cewa; "Azumtar ranar ar-fah ga wanda bai samu damar zuwa ai'kin hajji ba, yana kankare masa zunuban shekarar data gabata da shekarar daza tazo anan gaba".
@ﺻﺤﻴﺢ ﺍﻟﺠﺎﻣﻊ ﺑﺮﻗﻢ 3805.
Annabi Muhammad Sallallahu Alaihi Wasallam ya ƙara da cewa "Duk wanda ya azumci ranar ar-fa Allah ya gafarta masa zunubansa na shekaru guda biƴu, shekarar da ta gabata da wadda ta biyo bayanta)*
@ﺻﺤﻴﺢ ﺍﻟﺠﺎﻣﻊ ﺑﺮﻗﻢ 6335.
Kar amanta gobe ne tara ga watan Zulhajj, ranar da zata kasance ranar ar-fah, Allah ya bamu ikon azumtar yinin dake cikin wannan rana.
16/03/2023
Daga Kungiyar Marubuta AREWA WRINTERS ASSOCIATION OF NIGERIA(AWAN)
28/02/2023
RFI Hausa
Tayi Rashin Daya Daga Cikin Ma'aikatansu Wato Shehu Saulawa Allah Ya Jikanshi Da Rahama Yasa Kwaciya Hutu ce.
RFI Hausa ta yi rashin daya daga cikin zakakuran wakilanta wato Shehu Saulawa, wanda ya rasu a yammacin Litinin din nan a Asibitin Koyarwa na Tafawa Balewa da ke garin Bauchi na Najeriya bayan fama da jinya.
Za a yi jana'izarsa a gobe Talata da misalin karfe 9 na safe a Bauchi.
Allah Ya jikan sa. Allah Ya gafarta masa kurakuransa.
28/02/2023
Daga Dokin Karfe Tv
Dangane Da Zaben Nakeriya
Wanda Har Yanzu Ba'a Gama Tattara Sak**akon Zaben Sauran jahohi 9 Da S**a Rage
HALIN DA AKE CIKI: Zuwa yanzu INEC ta karɓi sak**akon jihohi 28, saura jihohi 9 kenan
A guda 28 ɗin nan; Asiwaju na da ƙuri'u 7,650,826
Atiku na da ƙuri'u 6,085,523
Jihohin da Asiwaju ya ci su 9 ne; Ogun,Ekiti,Ondo,Oyo, Zamfara, Niger, Benue, Jigawa da kuma Kwara.
Atiku ya lashe jihohi 11; Osun,Bayelsa,Akwa Ibom,Adamawa, Gombe,Yobe, Kebbi,Kaduna,Katsina, Bauchi da kuma Sokoto.
Shi kuma raina k**a ka ga gayya Obi ya samu jihohi 8; Edo, Nassarawa,Enugu,Abia, Plateau, Cross River da kuma jihar Lagos.
Kwankwaso kuwa ya samu jiha ɗaya wato jihar Kano.
Sauran jihohin da s**a rage inda komai zai iya faruwa sune Imo, Taraba, Delta, Rivers, Abuja, Ebonyi, Anambra, Borno da kuma jihar Kogi.
Magana ta gaskiya gadukkan alamu Tinubu ne da Nasara.
16/02/2023
Kuji Da Kyau Kuma Ku Sani
Abunda ya k**ata kowa ya sani Game da tsoffin kudi......
Bayan sanarwar da CBN ya bayar shekaran jiya na hana Bankuna karbar tsoffin kudi a yau shima shugaban kasar Najeriya Muhammadu Buhari ya kara tabbatar da hakan amma ya bada umurnin a cigaba da karbar iya tsohuwar 200 kadai inda ya umurci 'yan Najeriya da su gaggauta su maida tsoffin kudaden su CBN.
Kada ku manta CBN sun fara karbar tsoffin kudi tun a jiya Laraba sunce za su rufe karba daga gobe jumma'a.
Kusan duk ko'ina an daina karbar tsoffin kudade sai wurare 'yan kadan wasu jihohin tuni ko'ina an daina karba, duk da umurnin da wasu gwamnonin jihohi s**a bayar.
Abunda ya k**ata mu sani mu kuma kiyaye shine duk wanda kuka ga yana karbar tsoffin kudi to tabbas CBN zai kai su, CBN sunce daga gobe jumma'a za su rufe kuma bawai da zaran mutum yakai CBN a take zasu tura mishi kudin shi ba, dole sai sun dauki tsawon lokaci kafun su turawa Mutane kudin da s**a kai wanda a kalla zai iya kaiwa makonni ko wata ko sama da haka.
Sannan ya k**ata mu sani duk umurnin da Gwamnoni suke bawa al-ummar jihohinsu na su cigaba da karbar tsoffin kudi, duk wanda ya karba ya tara su a wurin shi har CBN s**a rufe daina karbar tsoffin kudi ya sani cewa fa babu wani gwamnan da zai chanja mishi kudinshi karshe dai sai dai asara tahau kanshi shi kadai don haka ya k**ata mu kiyaye.
✍️ Comr Abba Sani Pantami
16/02/2023
Ya Ake Ciki Dangane Da Rashin Karban Tsofaffin Kudaden Nigeria
Yan Najeriya da Dama Sun Shiga Cikin Wani Hali Na Rashin Samun Isassun Sababbin Kudade .
Shi Mi Yajawo Wannan Matsalar Muna Jiran Ra'ayoyinku
Cliquez ici pour réclamer votre Listage Commercial.
