UMAR FARUQ
MUSULUNCI SHINE ADDININU
14/01/2026
AN GUDANAR DA ZIKIRAR SHAHID IS'HAQ BIRNIN TAREDA SHEK ABUBAKAR NUHU TALATA MAFARA.
09/01/2026
TAREDA 'YAN UWA MUSULMI AL-MAJIRAN SHEIKH IBRAHIM ZAKZAKY (H), NA DA'IRAR MAFARA.
Alhamdulillah Yau Muna 20-Rajab-1447.
'yan uwa Musulmi al-majiran Sheikh Ibrahim Zakzaky (H), DANDALIN MATASA, NA IMAM ALI AR'RIDAH (A.S), s**a Fito Muzaharar Mauludin Imam Ali (A.S).
Kamar yadda aka Saba gabatarda wan nan Muzaharar Karkashin kulawar Matasa. Yanzu haka Muzaharar tana tafiya cikin tsari👇👇👇
01/01/2026
JAGORA (H) YA JA HANKALIN YARA AKAN KULA DA KARATU
Daga Ofishin Shaikh Ibraheem Zakzaky (H)
Da yake jawabi ga ƙananan yara, daliban makarantun Firamare da na Sakandare, waɗanda s**a shiga taron IVC a makon da ya gabata a Abuja, Jagora Shaikh Ibraheem Zakzaky (H) ya jaddada musu buƙatar dagewa da karatu da rage biye wa wasanni.
Shaikh Zakzaky, wanda ya gana da yaran a ranar Litinin 9 ga watan Rajab 1447 (29/12/2025) a gidansa da ke Abuja, ya ja hankalin iyayen yara akan kula da tarbiyar yaransu tun suna ƙanana, inda yace: “Tarbiya muhimmin abu ne, in aka bari mutun ya girma ba tare da shi ba, shikenan an lalata masa yarintarsa.”
Da yake magana da yaran, ya bayyana lokacin da ake shirya musu karatuttukan IVC a matsayin muhimmin lokaci. Yace: “Za ku yagi abinda za ku yaga ne (na ilimi). Kuma duk IVC ya kamata kar a bar mutum a baya. Kada ya yi wannan, ya zama na gaba ba zai zo ba.”
Ya kara da cewa: “Banda IVC kuma kamar yadda nace, iyaye kuma su lura da yara su rika karatu a gida, domin na makaranta (kawai) bai wadatar ba, na wajen IVC ma (kawai) bai wadatar ba.”
Jagoran ya ja hankali kan yadda ake da hanyoyin sadarwa a yanzu, yace, kar mutum ya riƙa ɓata lokacinsa a kalle-kallen wasanni, da abubuwa masu shagaltarwa. “Ya kamata su zama abubuwa ne na neman ilimi.”
A nan ne ya kwadaitar da su muhimmancin dogaro da littafi, fiye da dogaro da na'urorin Computer da waya, ko da da nufin neman ilimi ne. Inda ya bayar da misali da wani karin maganar Larabawa da ke cewa: “Mafi alherin abokin zama shi ne littafi.” Don haka ya buƙaci su zama masu lizimtar bugaggen littafi don karatu.
A karshe, Jagora ya jaddada kira ga daliban akan kulawa da karatu. Inda yace: “A kula da karatu, a yi ta karatu, ya zama baku da wani aiki sai karatu, karatu, karatu, karatu, ai tata yi, ai tata yi, ba ƙaƙƙautawa, shi ne nan-gaba ɗinku. In kaga lalataccen tsoho, to lalataccen yaro ne ya cigaba. In kaga mutumin kirki, to yaron kirki ne. Saboda haka tun yanzu ai ta karatu, ai ta karatu. Allah Ya ba da sa'a. Insha Allah.”
01/01/2026
#
01/01/2026
🌹 NASIHAR MU TA YAU LARBA 🌹
AL-HADIS👌
“Kuji tsoron saɓa wa Allah a ɓoye domin mai ganin ɓoyen shine zai yi hukunci ranar ƙiyama.”
__Imam Ali (As)
🌹🌹🌹
KAI TSAYE DAGA DA,IRAR TALATA MAFARA WAJEN TUNAWA DA WAKI,AR BUHARI TA 2015.
Click here to claim your Sponsored Listing.
