Daga Zuciyar Bintu

Daga Zuciyar Bintu

Share

Ina kawo muku labaran rayuwa kamar yadda suke. Ba Kari, ba ragi. Na ji na gani…Zan fada!

29/06/2026

LABARIN YADDA AKA CI ZARAFIN MARYAM AKAYI MATA FYADE WANDA HAR HAKAN YAYI SANADIYYAR RASA RAYUWARTA...

Maryam da ta kasance karamar yarinya yar aji biyu a karamar sakandire wato (JSS 2) a karamar hukumar kaugama dake jihar jigawa, kullun da daddare Maryam na zuwa gidan makota domin tayasu kwana inda anan ne dukkan lamarin ya faru..

Ya kasance a gidan akwai wani matashi mai suna Basiru, yanada aure harda yaya guda biyu, Basiru wanda akafi sani da Basiru Rabwal ya kasance yana satar hanya domin shiga dakin da Maryam take kwana sannan yayi mata fyade, yaci zarafinta, idan ya gama kuma yayi mata barazana cewa duk sadda ta kuskura na fadawa wani abunda ke faruwa tsakaninsu to tabbas saiya kasheta (threatening with murder), cikin tsoro da tsananin furgici haka Maryam ta kasa sanar da kowa halin da take ciki, shikuma Basiru ya cigaba da keta mata haddi da cin zarafinta har saida yakai Maryam ta fara rashin lpy, bayan da Maryam ta fara jinya ne Mahaifiyar Maryam ta kaita asibiti domin sanin abunda ke damun yarinyar, anan ne fa aka sanar da Mahaifiyar cewa Maryam na dauke da juna biyu (early adolescent pregnancy) saboda Maryam batakai shekara sha takwas a duniya ba, hakan ya tada hankalin Mahaifiyar Maryam sosai inda har yakai ga ta yanke jiki ta fadi, daga baya dai sun kasa daukar wani mataki akan abun sakamakon cewa Mahaifin Maryam yace babu ruwanshi sannan mahaifiyar Maryam na tsoran sanarwa duniya halin da yarta take ciki domin suna tsoran bata suna ko abun kunya, an amince cewa idan Maryam ta haihu to dole zaa aurama basiru ita..
Maryam ta cigaba da dawiniya da ciki har zuwa lokacin haihuwa, inda ta fada cikin lalurar rashin jini wato Maternal Anemia wanda hakan na iya faruwa sakamakon dauka ciki da tayi ba tare da shekarunta sunkai lokacin ba (early adolescent pregnancy), anyi kokarin ceto rayuwar Maryam a asibitin Hadejia dake Jihar Jigawa amma hakan bai yiwu ba, inda Maryam ta rasa rayuwarta a wajen haihuwa, bayan rasuwar Maryam an ceta jaririn dake cikin ta hanyar yi mata CS..
Daga karshe dai Maryam ta rasa rayuwarta a ranar lahadi 10 ga watan May na wannan shekarar ta 2026 sanadiyyar cin zarafi da keta haddi da Basiru yayi mata, wanda hakan yayi sanadiyyar dauki cikin da yakai ga ta rasa rayuwarta, rasuwar Maryam ta auku ne sakamakon zalunci, keta haddi da kuma cin zarafi, domin munsan cewa daukar ciki batare da shekarun yarinya sunkai ba ka iyayin sanadiyyar rayuwarta a wajen haihuwa, wanda mukafi sani da high mortality rate as a result of early adolescent pregnancy.
A yanzu haka iyayen Maryam na cigaba da jimamin rashin yarsu Maryam cikin halin rashin wanda zai tsaya musu domin kwatawa Maryam hakkinta ta fuskar shari'a, a inda a gefe daya kuma Basiru ya kwashe matarsa da yayansa zuwa kano domin cigaba da rayuwa cikin walwala da jin dadi..

wannan shine labarin yadda cin zarafin Maryam ya kasance da kuma yadda Maryam ta rasa rayuwarta a sanadiyyar hakan.
Muna fatana zaa tsayawa Maryam domin ganin cewa anyima iyayenta adalci dukda Maryam bata raye, Muna fatan Adalci zaiyi Nasara, Amin

Want your business to be the top-listed Beauty Salon in Abuja?
Click here to claim your Sponsored Listing.

Category

Website

Address

Abuja

Opening Hours

Tuesday 09:00 - 17:00
Friday 09:00 - 17:00