Rigar So

Rigar So

Share

Rigar So page ne wanda zai dinga zantawa da masoya kamar! Samari, Yan Mata da Zawarawa

24/11/2025

Wannan shafi mai albarka na -so yana tir da Allah wadai da halin wannan Amarya wacce ta yanke mijinta yankan rago a Jihar Katsina.

wannan Amarya bata yi tunani ba sam sannan bata kyauta ba sam, sannan daraja da kima da mutuncin ta sun ragu ga al'umma, sannan muma a wannan shafin namu bata yi amfani da Rigar so ba tayadda yadace domin mu a Rigar so muna yi mata lakabin cireta sai da dabara.

Allah ya jikan sa da rahama tare da sauran wadanda s**a rigamu gidan gaskiya .

17/11/2025

Son Shi ne Ya Jijjiga min Zuciya ta❤️❤️❤️

Hmmmm lallai ma rigar So haka take cireta sai da dabara, na kaɗu sosai a duk lokacin da zuciyata ke bugawa yabon sa take, dai dai da second guda zuciyata bata daina ambaton sa amma a haka ya cakamin kibiyar ajali a zuciyata bai kallona koda da second ɗaya domin inji daɗi kullum sai azabtar dani yake yi.

Ga shi ba zan iya kai ƙararsa ba saboda son sa kullum daɗa jijjiga min zuciyata yake idanuwa kullum cikin zub da ruwan hawaye suke, ga shi kuma ban san damuwar sa ko ɗaya, a don haka nake neman shawarar ku yan'uwa na Mata ta wacce hanya zan magance wannan matsalar?

Ku cigaba da yi mana comment da like da share a wannan sabuwar tashar ta mu akwai kyauta me tsoka ga wanda yafi samun like, sannan idan kuna da bukatar hira damu kuyi mana message ta Facebook domin ji ko ya Rigar so take a wajen ku?

IZZAR SO TV soyayya ruwa zuma TARKON KAUNA BY MUSTY PABAH

Website