Kasida Spotlight

Kasida Spotlight

Share

Contact information, map and directions, contact form, opening hours, services, ratings, photos, videos and announcements from Kasida Spotlight, Health/Beauty, T/D, Gusau.

10/07/2026

🌙 BARKA DA JUMA'A 🌙

Kungiyar KASIDA SPOTLIGHT tana mika sakon Barka da Juma'a ga Grand Patron É—inmu, Hon. Shamsu Kasida.

Muna addu'ar Allah (SWT) Ya karɓi ibadunmu, Ya ƙara maka lafiya, hikima, ɗaukaka da albarka. Ya ci gaba da yi maka jagora a dukkan al'amuranka, Ya sa wannan rana ta Juma'a ta kasance alheri da rahama gare ka da iyalanka da mu Baki Daya.

Juma'a Mubarak.

08/07/2026

Hajiya Habiba shehu danfulani (Lu'u'Lu'un matan kasar Hausa)

06/07/2026

LU'U'LU'UN CE A CIKIN MATA

Wannan aiki da Hajiya Habiba Shehu Danfulani (Lu'u'Lu'un Matan Gusau) shugabar ZamCare Initiative ta gudanar na samar da rijiyoyin ruwa na zamani, wanda Hon. Shamsu Kasida ya jagoranta, tabbas abin a zo a gani ne.

Abin lura a nan shi ne, Hajiya Habiba Shehu Danfulani ta zo da sabon tsari mai É—orewa wanda ya bambanta da abin da aka saba gani. Ta yi tunani, ta yi nazari mai zurfi, sannan ta fito da shirin da manufarsa ita ce ci gaban Jihar Zamfara da walwalar al'umma. Wannan wani aiki ne wanda, kaf a cikin matan 'yan majalisu waÉ—anda s**a gabata da na yanzu, babu wadda ta zo da kwatankwacin wannan tsari sai Hajiya Habiba Shehu Danfulani, Lu'u'Lu'un Matan Gusau.

Wannan aiki ya nuna cewa ruwa ba kawai abin sha ba ne, rayuwa ne; kuma jagoranci na gari shi ne wanda yake kawo sauyi da amfani ga jama'a ba tare da hayaniya ko yaudara ba.

Saboda wannan hangen nesa da aikin alheri, al'ummar Zamfara suna da dalilin cewa Hajiya Habiba Shehu Danfulani "(Lu'u'Lu'un ce a cikin mata)," mace mai tausayi, hikima da kishin talakawa.

Allah Ya sakawa Hajiya Habiba Shehu Danfulani da mafificin alheri, Ya ƙara mata lafiya, hikima da ikon ci gaba da hidimtawa al'umma da kawo sabbin tsare-tsare, kamar yadda take fata. Amin.

KASIDA SPOTLIGHT

05/07/2026

President
Governor
2031, in Sha Allah

04/07/2026

GIDAUNIYAR ZAMCARE TA SAMAR DA RIJIYOYIN MURTSATSE GUDA BIYAR A GUSAU

Shugabar ZamCare Initiative Zamfara State, Hajiya Habiba Shehu Danfulani (Lu'u'Lu'un Matan Gusau), ta samar da rijiyoyin murtsatse na zamani guda biyar (5) domin magance matsalar ƙarancin ruwa a wasu unguwanni na Garin Gusau.

Unguwannin da s**a amfana sun haɗa da: • Unguwar Dan Baba Tsunami
• Bulunku
• Samunaka
• Unguwar Matawalle
• Gidan Dutsi

Wannan na daga cikin manyan manufofin Gidauniyar ZamCare Initiative, wadda aka kafa domin gudanar da ayyukan jin ƙai da ci gaban al'umma ba tare da wata manufa ta siyasa ba.
Tun bayan ƙaddamar da gidauniyar, an aiwatar da ayyuka da dama da s**a haɗa da tallafin marayu da masu ƙaramin ƙarfi, gyaran makarantun Islamiyya, rabon littattafan ilimi, tallafin lafiya da kuma samar da ruwan sha ga al'umma.

Allah Ya saka Hajiya Habiba Shehu Danfulani da mafificin alheri, Ya ƙara mata lafiya, hikima da ikon ci gaba da hidimtawa al'umma. Amin.

Kasida Spotlight.

Photos from Kasida Spotlight's post 04/07/2026

Hajiya. Habiba Shehu Danfulani
(Lu'u Lu'un Matan Gusau) âś…

04/07/2026

MAI GIRMA SANATA ABDUL'AZIZ YARI YA ZIYARCI ASAD HEALTH MEDICINE

Mai Girma Sanata Abdul'aziz Yari Abubakar ya kai ziyarar ban girma zuwa Asad Health Medicine da ke Kaduna, cibiyar da ke ƙarƙashin jagorancin Hon. Abdulmalik Zubairu Zannan (Zannan Bungudu).

A yayin ziyarar, ya sanya albarka tare da yi wa cibiyar da masu gudanar da ita fatan alheri da ci gaba mai É—orewa.

Allah Ya ƙara wa Mai Girma Sanatan lafiya, ɗaukaka da albarka, Ya kuma sanya wannan ziyara ta zama alheri ga kowa. Amin.

Kasida Spotlight.

03/07/2026

Hon. Shamsu Kasida đź’™

Grand patron
Kasida Spotlight
Leadership with Integrity

02/07/2026

Alhamdllah 🤗🙏

01/07/2026

Allah Ka Amintarda Maigirma Zannan Bungudu Ka tabbatar Muna da Alhairi, Albarkar Alqur'ani 🤲

Want your business to be the top-listed Beauty Salon in Gusau?
Click here to claim your Sponsored Listing.

Category

Website

Address

T/D
Gusau