Garewa TV

Garewa TV

Share

online TV

24/09/2026

Jawabin mataimakin shugaban kasar nigeria kenan Sen. Khashim Shattima a wajen taron Majalisar Dinkin Duniya Da yake gudana a New York ta kasar America.

Photos from Garewa TV's post 16/09/2026

Jiragen sama na ƴan kasuwa za su fara zirga-zirga a filin jirgin Gusau a Oktoba

​Ana sa ran fara tashi da saukar jiragen sama na cikin gida da na ƴan kasuwa a filin jirgin sama na ƙasa da ƙasa da ke Gusau a watan Oktoba mai zuwa, yayin da hukumar hula da sufurin jiragen sama ta ƙasa (NCAA) ta gudanar da cikakken binciken gani-da-ido kan shirye-shiryen da ake yi.

​Kwamishinan ayyuka na jihar Zamfara, Lawal Barau Bungudu, ne ya jagoranci jami’an na NCAA da ƙwararrun injiniyoyi na ma’aikatar domin duba kayan aiki, matakan tsaro, da kuma cikakken shirin filin jirgin na gudanar da sufuri mai aminci da nagarta.

​A cikin wata sanarwa da jami’in yaɗa labarai na ma’aikatar Jamilu Bello, ya fitar, ya bayyana cewa wannan ziyara ta nuna wani muhimmin mataki ne a ƙoƙarin da gwamnatin Dauda Lawal ke yi tare da haɗin gwiwar hukumomin sufurin jiragen sama domin tabbatar da cika dukkan sharuɗɗan da doka ta tanada kafin a buɗe filin ga al'umma.

05/09/2026

Saimun fara gyara zukatanmu da halayanmu kafin Allah ya gyaramana,

Kadan daga cikin Yankin khudbar Jumu'a Mai taken Harsai kungyara kafin Allah ya gyaramaku.

Photos from Garewa TV's post 03/09/2026

JARIDAR DAILY TIMES TA KARRAMA GWAMNA DAUDA LAWAL A BUKIN CIKARTA SHEKARA 100

Gwamnan Jihar Zamfara, Dauda Lawal, ya karɓi lambar yabo ta Gwamna Mafi Fice daga jaridar Daily Times a yankin Arewa maso Yamma, yayin bikin cika shekaru 100 da kafuwar jaridar da aka gudanar a Abuja.

Gwamnan ya karɓi lambar yabon ne a yau a wajen bikin DTN@100 Times Heroes Awards, wanda jaridar Daily Times, wadda ita ce jarida mafi daɗewa a Najeriya, ta shirya domin bikin cika shekaru 100 da kafuwarta.

An karrama Gwamna Lawal ne saboda jagorancinsa, hidimar jama’a da kuma gudunmawar da yake bayarwa wajen ci gaban ƙasa.

Lambar yabon na daga cikin shirye-shiryen bikin cika shekaru 100 na jaridar, wadda aka fara bugawa a shekarar 1926, kuma ta kasance tana rubuta tarihin ci gaban Najeriya ta fuskar siyasa, tattalin arziki, zamantakewa da al’adu tsawon ƙarni guda.

Shugaban Majalisar DTN@100 Heroes Awards, Bolaji Okusaga, ya bayyana cewa an zaɓi Gwamna Lawal ne saboda ya samu mafi yawan ƙuri’un gabatar da sunaye a yankin Arewa maso Yamma.

Ya ce:

“Bayan gudanar da cikakken tsarin gabatar da sunaye da kuma kaɗa ƙuri’a daga jama’a, ka samu mafi yawan ƙuri’u a wannan rukunin na lambar yabo.

“Daga bisani, Majalisar Times Heroes Award da sauran muhimman masu ruwa da tsaki sun tabbatar da zaɓenka, bisa la’akari da jagorancinka, hidimar jama’a da kuma gudunmawarka wajen ci gaban ƙasa,” in ji Mista Okusaga.

Gwamna Lawal ya bayyana godiyarsa ga Hukumar Daraktoci, Masu Gudanarwa da Kwamitin Shirya bikin Daily Times Nigeria @100 Celebration, da Majalisar Times Heroes Award, da kuma dukkan ‘yan Najeriya da s**a mara wa takararsa baya.

Ya bayyana cewa wannan karramawa ta nuna irin jajircewarsa wajen inganta shugabanci na gari da kuma samar da ingantaccen aikin yi wa jama’a hidima a Jihar Zamfara.

Sauran fitattun ‘yan Najeriya da aka karrama sun haɗa da Sakataren Gwamnatin Tarayya (SGF), Sanata George Akume, da kuma tsohon Shugaban Bankin Raya Afirka (AfDB), Dr. Akinwumi Adesina.

Jaridar ta sanar da cewa za a saka sunayen waɗanda s**a karɓi lambobin yabo na DTN@100 Times Heroes Awards cikin fitattun mutane da cibiyoyin da s**a fi taka muhimmiyar rawa, a cikin littafin Nigerian Grand Book mai shafuka 700.

“Wannan littafi zai kasance kundin tunawa na ƙasa, tare da zama tarihi na dindindin game da mutane, cibiyoyi da nasarorin da ke taka rawa wajen tsara ci gaban Najeriya.”

Shugaban Ƙasa, Bola Ahmed Tinubu, ne ya rubuta gabatarwar littafin Nigerian Grand Book.

SULAIMAN BALA IDRIS
Mai Magana da Yawun Gwamnan Jihar Zamfara
3 ga Satumba, 2026

30/08/2026

Sha'anin Siyasa a Nigeria daga bakin malamai.

29/08/2026

"Mutanen kauyukkan Shagari da Bukkuyum zakuji karar boma-bomai a wasu jirage ukku masu yawo. Sun darje sansanin Yanta'adda a dajin Shagari, sun darje na kauyukkan Bukkuyum a Gizazza. Don haka mutane su daina zirga-zirga cikin daji har sai anga yadda Hali yayyi. Wadanda ke zaune kusa ga Gizazza zasuga wuta da hayaki na tashi saboda anyi (Operation No living thing) An darje bandits hadda Shanun satar da s**a Tara a wurare da dama".

© Umar Gidado Gummi

Photos from Garewa TV's post 28/08/2026

Sojojin Operation FANSAN YAMMA sun gano tare da lalata bam ɗin IED da ’yan ta’adda s**a dasa a Jihar Zamfara

Rundunar Operation FANSAN YAMMA ta samu nasarar gano tare da lalata wani bam ɗin IED da ’yan ta’adda s**a dasa a kan hanyar Gurusu–Gwashi, a ƙaramar hukumar Bukkuyum ta Jihar Zamfara, a ranar 27 ga Agusta 2026.

Bayan samun sahihin bayanan sirri, dakarun Sector 2 sun gaggauta kai ɗauki, s**a killace yankin tare da tabbatar da cewa ƙwararrun jami’an EOD sun lalata bam ɗin cikin aminci. Daga bisani, sojojin s**a ci gaba da sintiri domin hana ’yan ta’adda samun damar kai hare-hare.

Wannan nasara ta nuna ƙudurin Operation FANSAN YAMMA na kare rayukan jama’a, da kiyaye muhimman hanyoyi, da kuma dakile dabarun ’yan ta’adda.

Rundunar ta buƙaci jama’a su kasance cikin taka-tsantsan tare da kai rahoton duk wani abu ko motsi da ake zargi ga hukumomin tsaro cikin gaggawa, domin bayanan jama’a na taimakawa wajen hana hare-hare da ƙara tsaron al’umma.

Rahotanni sun tabbatar da cewa hare-haren ’yan fashi a Zamfara sun haɗa da kisa, satar mutane da kuma fyade.

Photos from Garewa TV's post 28/08/2026

Sojojin najeriya sunyi nasarar fatattar yan ta'adda a garin ra6a ta jahar sokoto.

Want your business to be the top-listed Beauty Salon in Gusau?
Click here to claim your Sponsored Listing.

Category

Website

Address

Bye Pass Adjacent Karma Guest Inn
Gusau

Alerts

Be the first to know and let us send you an email when Garewa TV posts news and promotions. Your email address will not be used for any other purpose, and you can unsubscribe at any time.

Subscribe

We will notify you when anything happens in Gusau.