Vision FM Kano

Vision FM Kano

Share

VISION FM KANO 92.5
SAMAR MUKU DA SAHIHAN LABARAI A KODA YAUSHE SHINE MURADIN MU. MIKIYA MAI HANGEN NESA

29/09/2026

Na dawo cikin ƙoshin lafiya, sannan a shirye nake in koma bakin aiki gadan-gadan.

Bola Ahmad Tinubu
Shugaban Najeriya

Me zaku ce?

29/09/2026

Rundunar ’Yan Sandan Jihar Borno ta k**a tare da gurfanar da wasu mutane biyar a Maiduguri, bisa zargin bugawa da kuma sanya rigunan da ke ɗauke da rubutun Tinubu Must Go.
‎
‎Waɗanda aka k**a sun haɗa da Baba Aji Gremami mai shekaru 44, Mustapha Abba Yemen mai shekaru 28, Abbacha Mohammed Ali mai shekaru 32, Adam Umar Gubio mai shekaru 21 da Abdulhamid Mohammed mai shekaru 21. Rahoton farko na ’yan sanda ya ce an k**a su ne ranar 25 ga Satumba da misalin ƙarfe 11 na safe a yankin West End Roundabout da ke Maiduguri.
‎
‎’Yan sandan sun tuhumi mutanen da laifukan haɗa baki wajen aikata laifi, tunzura jama’a, tayar da hankalin jama’a da kuma daba, bisa wasu sassa na kundin dokokin Jihar Borno.

29/09/2026

‎Shugaban Ƙasa Bola Ahmed Tinubu ya isa birnin Lagos bayan kammala hutun aikinsa a ƙasar Faransa. Shugaban ya sauka ne a sashen filin jirgin saman Murtala Muhammed na musamman da ke Ikeja a ranar Talata, inda Gwamnan Jihar Lagos, Babajide Sanwo-Olu, da wasu manyan jami’ai s**a tarbe shi.
‎
‎Tinubu ya bar Abuja a ranar 30 ga watan Agusta, inda ya fara ɗan lokaci a Landan kafin ya wuce Paris. A cewar Fadar Shugaban Ƙasa, Tinubu ya bar Paris zuwa Lagos ne domin gudanar da wasu muhimman taruka da shugabannin siyasa da abokan hulɗarsa a cikin kwanaki masu zuwa.
‎
‎Fadar Shugaban Ƙasar ta ce Shugaban ya zaɓi zuwa Lagos ne da farko domin girmama marigayi Cif MKO Abiola, wanda ya lashe zaɓen Shugabancin Najeriya na watan Yunin 1993 kuma ya taka muhimmiyar rawa a gwagwarmayar dimokuraɗiyyar ƙasar. Ana sa ran Tinubu zai halarci bikin ƙaddamar da wani fim da aka shirya domin girmama Abiola a ranar 1 ga Oktoba, Ranar ’Yancin Najeriya, a gidan wasan kwaikwayo na Wole Soyinka da ke Iganmu, Lagos.

29/09/2026

Indai dan majalisar jiha na Tarauni za'a shiga dashi zabe toh tabbas jam'iyyar APC zata faɗi zabe a ƙaramar hukumar Tarauni saboda babu abunda yakeyi a majalisa.

29/09/2026

Rundunar Sojin Najeriya ta kaddamar da sabbin motocin yaƙi masu sulke da wasu sabbin rundunonin soji guda uku a Jihar Kebbi, a wani mataki na ƙara ƙarfafa ayyukan tsaro a yankin Arewa maso Yammacin ƙasar.
‎
‎Babban Hafsan Sojin Najeriya, Laftanar Janar Waidi Shaidu, ya kaddamar da Rundunar 28 Armoured Brigade da Garrison a Birnin Kebbi, da motocin yaƙi masu sulke 281 a Yauri, da kuma Sashen Mak**ai na 381 a Kaoje. Sai dai ya samu wakilcin Manjo Janar Bemgba Paul Koughna, Kwamandan Runduna ta 8 ta Sojin Najeriya kuma Kwamandan Sashe na Biyu na Rundunar Hadin Gwiwa ta Arewa maso Yamma, Operation FANSAN YAMMA.
‎
‎Koughna ya ce sabbin rundunonin za su faɗaɗa ayyukan sojoji, ƙarfafa sa ido da kuma rage lokacin da ake ɗauka wajen mayar da martani ga barazanar tsaro. Ya kuma umarci Mukaddashin Kwamandan Rundunar 28 Brigade, Kanal Abdullahi Umar, da ya tabbatar da samar da isasshen ƙarfin tallafin mak**ai ga ayyukan sojin da ake gudanarwa, musamman domin dakile ayyukan ƙungiyoyin masu ɗauke da mak**ai da sauran barazanar tsaro a Jihar Kebbi.

29/09/2026

Gwamnatin Jihar Jigawa ta ware Naira biliyan 1.337 domin inganta kayan aikin Gidan Rediyon jihar da kuma gina sabbin tashoshin rediyon FM guda biyar. Za a gina tashoshin a ƙananan hukumomin Gumel, Gwaram, Hadejia, Kazaure da Ringim.
‎
‎Kwamishinan Yaɗa Labaran Jihar, Sagir Musa Ahmed, ya bayyana hakan ne bayan taron Majalisar Zartarwar jihar da aka gudanar ranar Litinin, 28 ga Satumba 2026. Ya ce majalisar ta amince da samarwa da girka na’urar 50KW Harris Digital AM a Jigawa Radio, tare da na’urorin 3KW FM Transmitters ga sabbin tashoshin guda biyar.
‎
‎Ayyukan sun kuma haɗa da samar da kayayyakin yaɗa shirye-shirye domin inganta inganci da ƙarfin isar da shirye-shiryen rediyo. Gwamnatin ta ce sabbin tashoshin za su taimaka wajen faɗaɗa isar shirye-shiryen rediyo ga al’ummar jihar Jigawa.

29/09/2026

Wani rahoto na Babban Bankin Ƙasashen Yammacin Afirka masu amfani da kuɗin CFA, BCEAO, ya nuna cewa Nijar na kan gaba wajen haɓakar tattalin arziƙi a tsakanin ƙasashe mambobin ƙungiyar UEMOA.
‎
‎Rahoton ya nuna cewa Nijar ce ke da mafi girman haɓakar tattalin arziƙi a tsakanin ƙasashen da ke cikin ƙungiyar, bisa bayanan da bankin ya fitar.
‎
‎Ƙungiyar UEMOA ta ƙunshi ƙasashen Yammacin Afirka da ke amfani da kuɗin CFA, yayin da rahoton BCEAO ya mayar da hankali kan yanayin haɓakar tattalin arziƙin ƙasashen mambobin ƙungiyar.

29/09/2026

Farfesa Isa Ali Ibrahim Pantami ya lashe sabon zaɓen fidda gwani na jam’iyyar PDP a Jihar Gombe, inda ya samu ƙuri’u 817 cikin ƙuri’u 1,020 da aka kaɗa.
‎
‎Khamisu Ahmed Mai Lantarki ya samu ƙuri’u 153, yayin da Aliyu Usman Gari ya samu ƙuri’u 50. Jimillar ƙuri’un da aka kaɗa sun kai 1,020.
‎
‎An gudanar da sabon zaɓen ne biyo bayan umarnin kotu na sake gudanar da zaɓen fidda gwani na jam’iyyar PDP a Jihar Gombe.

29/09/2026

Gwamnan Kano, Abba Kabir Yusuf, ya nemi Majalisar Dokokin Jihar Kano ta amince da ƙarin kasafin kuɗi da gyaran kasafin shekarar 2026 na sama da Naira tiriliyan 1.2. An gabatar da buƙatar ne cikin wasiƙar da Kakakin Majalisar, Isma’il Falgore, ya karanta yayin zaman majalisar na ranar Talata.

Gwamnan ya ce an buƙaci ƙarin kasafin ne sak**akon ƙarancin kuɗaɗen da jihar ke samu daga Asusun Tarayya, biyo bayan aiwatar da sabuwar dokar haraji. Ya ce jihar ta yi hasashen samun ƙarin kuɗaɗe daga Asusun Tarayya, ciki har da VAT, amma wasu kuɗaɗen shiga k**ar signature bonuses, exchange differences da NNPC refunds suna hannun Gwamnatin Tarayya.

Shirin ya tanadi Naira biliyan 45 a matsayin ragowar kuɗaɗen da aka shigo da su, Naira biliyan 753.44 na kuɗaɗen shiga na yau da kullum, da Naira biliyan 402.82 na kuɗaɗen manyan ayyuka. Jimillar kuɗin da ake sa ran samu ita ce Naira tiriliyan 1.201, inda Naira biliyan 390.31 za su tafi kan ayyukan yau da kullum, yayin da Naira biliyan 810.95 za a kashe wajen ayyukan raya ƙasa. Majalisar ta miƙa ƙudurin ga Kwamitin Dokoki da Harkokin Kasuwanci domin ci gaba da nazari kafin ɗaukar matakin doka.

29/09/2026

Me kuke fata bayan dawowar shugaban kasa Bola Ahmad Tinubu daga hutun da ya tafi?

Ku bayyana mana ra'ayoyin ku ⤵️⤵️⤵️

Want your business to be the top-listed Beauty Salon in Kano?
Click here to claim your Sponsored Listing.

Address

Guda Abdullahi
Kano
700101