Faisal Saifullahi
Contact information, map and directions, contact form, opening hours, services, ratings, photos, videos and announcements from Faisal Saifullahi, Mlf, Katsina.
23/05/2025
Tunda safe babu abinda naci Sai Ledan taliya 2 da Tea☕ and bread🍞 da wata Yar doya da indomie🍝 da kwai guda 8 nayi maleji.🥹🚶🏻
21/08/2024
Cikakken bayani akan yadda Gasar zakarun nahiyar Turai 2024/25 zata gudana.
An sauya fasalin yadda gasar zakarun nahiyar Turai (Champions League) ta wannan kakar zata kasance, domin cigaba da nishaɗantar da ƴan kallo, ƴan wasa, da kuma ƙungiyoyi.
Yaya tsarin yake? Kuma ta ya hakan zai amfanar ga masoya mafi kyawun wasa na duniya? Bari mu je dalla-dalla cikin bayanan.
Kamar yadda muka sani, za a samu sauyin wasu abubuwa a gasar zakarun Turai. Daga wannan kakar babu batun raba ƙungiyoyi daga Rukunin A zuwa H kamar yadda aka saba raba su duk kakar wasa, sannan kuma an ƙara yawan ƙungiyoyin gasar daga 32 zuwa 36, za a fitar da babban teburi guda ɗaya, daga na farko har zuwa na 36 duka zasu kasance a wannan teburin guda ɗaya.
Gasar zakarun Turai ta bana zata zo da bambanci kamar yadda muka shaida a baya. Zamu ga ƙungiyoyi 36 saɓanin yadda muka saba ganin ƙungiyoyi 32. Kuma duka zasu kasance a Teburi ɗaya. Amma kuma hakan bawai yana nufin kowacce ƙungiya zata kara da kowacce ƙungiya ba ne kamar yadda aka saba yi a Gasar Lig.
An ƙara yawan ƙungiyoyin zuwa 36 ne domin a ƙara faɗaɗa gasar sannan kuma a baiwa wasu ƙananun ƙungiyoyin dama waɗanda s**a fito daga ƙananun Lig a nahiyar Turai domin suma su fafata gasar. Amfanin hakan shine domin a ƙara haɓɓaka gasar kuma a kawo daidaito.
Saɓanin amfani da Rukuni-Rukuni, sabon salon gasar zakarun nahiyar Turai zai amfani da tsarin da bai kai wancan ba. Akan wannan tsarin, ƙungiyoyi 36 zasu kasance a babban Teburin Lig guda ɗaya, inda kowacce ƙungiya zata fafata wasanni takwas da ƙungiyoyi takwas mabanbanta, wasa huɗu a gida, wasa huɗu a waje. A baya mun san cewa idan AC Milan ta buga wasa da Real Madrid a Santiago, to Real Madrid zata bi AC Milan Sansiro domin buga wasa zagaye na biyu. Amma a wannan karon an canza tsarin hakan. Babu batun buga wasa gida da waje da ƙungiya ɗaya. Wannan karon idan kuka fafata wasa sau ɗaya shikenan, amma hakan zaiyi aiki ne kawai a matakin farko na gasar kafin a tsallaka zagayen Siri ɗaya ƙwale.
Dabarar yin wannan sabon canjin, wanda ya haɗa da yin Teburin Lig babba guda ɗaya shine: za a dinga fafata manyan wasanni da yawa. Misali, Real Madrid Vs Manchester City, ko FC Barcelona Vs Bayern Munich, duka zasu iya haɗuwa da juna tun a matakin Rukuni. Manyan ƙungiyoyi zasu kara da juna da yawa sosai ta wannan hanyar. A ƙalla wannan itace dabarar kawo sabon canjin. Hakan zaifi baiwa ƴan kallo nishaɗi da kuma ƙungiyoyin. Amma bayan haka, kowanne wasa a cikin takwas ɗin da zaka buga za a dinga lissafa shine kamar kana bugawa da ƙungiyoyi 36.
Ƙungiyar da tafi yawan maki itace zata kasance a gurbi na ɗaya, idan kuma maki yazo kai da kai, za a duba ƙungiyar da tafi yawan ƙwallaye. Idan hakan ma yazo ɗaya to za a duba ƙungiya mafi ƙarancin katin gargaɗi.
Bayan kowacce ƙungiya ta buga wasanni takwas, ƙungiyoyi takwas ɗin farko ne zasu wuce kai tsaye zuwa zagayen ƴan 16. Ƙungiyoyin da s**a kammala daga mataki na 9 zuwa na 24 zasu buga da junan su domin samun gurbi a mataki na gaba. Yayin da 8 daga cikin su zasu tsallaka zagayen ƴan 16. Ragowar kuma zasu koma gida. Wanda hakan ke nufin ƙungiyoyi 16 zasu fafata a matakin Siri ɗaya ƙwale. Ƙungiyoyin da s**a ƙarƙare daga na 25 zuwa na 36 sun fice daga gasar kai tsaye kuma bazasu buga gasar Europa League ba, zasu wuce gida ne kai tsaye.
UEFA ta ce: "A matakin tsallakawa zagayen ƴan 16. Ƙungiyoyin da s**a kammala daga mataki na 9 zuwa na 16 sune zasu fara karɓar baƙoncin ƙungiyoyin da s**a kammala daga na 17 zuwa na 24 a wasan neman gurbin tsallakawa zagayen ƴan 16. Kuma kowacce ƙungiya zata buga wasa ɗaya a gida ɗaya a waje. Ƙungiyoyi 8 ɗin da s**a samu nasara a cikin su sune zasu tsallaka zagayen ƴan 16, inda zasu fuskanci ƙungiyoyin da s**a kammala daga na farko zuwa na 8 a babban Teburin Lig ɗin gasar, inda za a raba jadawalin yadda zagayen zai kasance daga wannan lokaci." - Haka UEFA ta ce a (2024).
Babu canji a matakin Siri ɗaya ƙwale (zagaye na ƴan 16) za a cigaba da fafata shi kamar yadda tsarin sa yake a baya.
13/07/2024
NEW KIT'S 8 9 15
14/03/2024
R_______A_______M_______A________D_____A______N________🕋📿🌙___K________A_____R______E_______M_______
🕋______________♥️____________📿________🕌_______🌹_____________☘️_________🌙💞🔥♥️
01/01/2024
25/12/2023
Smile 😊 😊 😊
24/12/2023
mãñ øf thé pêöplē
22/12/2023
♥️♥️♥️mr❤️❤️mss✊✊❤️♥️ today the best kannywood celebrities 💋💋 with Hausa 📷 🙏💋🙏💚 📷📸💪✌️🥑✍️😜💚💋💋💯🙏✊💯j southern
21/12/2023
Click here to claim your Sponsored Listing.
Culinary Team
Attire
Contact the business
Telephone
Website
Address
Katsina
FRIENDS
