SUNNA TV

SUNNA  TV

Share

Alhamdulillahi wassalatu wassalamu ala sayyaduna s a w

04/30/2026
04/29/2026

Daga Bautar Dodo Ta Karbi Addinin Musulunci ☪️
Wata yarinya da aka sani da suna Bautan Dodo ta karɓi addinin Musulunci, duk da cewa iyayenta suna bautar dodo.

Yanzu tana makaranta a ƙarƙashin kulawar malamai da muka ajiye a garin.

Duk wanda yake son aurenta zai bi tsarin sadaki da aka tanada a addini kawai.

Bayan wannan, za a samar mata da sauran abubuwan da s**a dace don rayuwa cikin sauƙi, insha Allah.

Sakon Darasi
Karɓar addini cikin sanin makama da bin shari’a na da muhimmanci

Tabbatar da cewa a yi wa yara jagora da ilimi mai kyau domin tabbatar da rayuwa mai tsari
Duk wani yunkuri na aure ya kamata a yi bisa tsarin addini da shari’a

Allah Ya albarkaci rayuwarta, Ya shiryar da ita, Ya kuma sa kowa ya bi hanyar gaskiya 🤲

Photos from SUNNA  TV's post 04/29/2026

ALHAMDULILLAH, MAULANA YA SHIGA SABON AIKI

مركز الشيخ إبراهيم نياس للبحوث والوثائق

SHEIKH IBRAHIM NYASS CENTRE FOR RESEARCH AND DOCUMENTATION.

Allah Ya saka muku da alkhairi Maulana Prof. Ibrahim Maqari (H) Allah Ya iyamaku Ya qara karfafarku alfarmar Sayyiduna Rasulullahi ﷺ.

04/29/2026

sayyada
Nana
kodamaikarasamun sunan

Photos from SUNNA  TV's post 04/23/2026

Hotunan Tarin Wasu Mata Da S**a Shiga Musulumci Na Daukar Hankali a Soshiyar Midiya

Jajurtaccen sojan nan mai da'awar Musulumci, Adam Ashaka ne ya sanya hotunan matan da ya ce sun karbi Musulumci a hannunsa, inda ya shaida cewa yayi hoton ne a lokacin da basu kai ga karbar shahada ba, da kuma bay and da s**a musulumta. Allah ya taimaki gaskiya

04/23/2026

Haka Shehu Ɗanfodiyo ya zo ya samu dayawan al'ummarmu suna bautar dodo, cikin ikon Allah ya taimake shi ya tsamo su daga bautar dodo. Amma saboda rashin kunya wai yanzu shehun da ya tsamo kakanninsu daga wannan masifa shi ne abin zagi, da ba don Shehu ba da yanzu duka yara masu zagin nan su ma suna can suna bautar tsumburbura da dodo kuma suna shan burkutú.

Yanzu fa kamar haka ne, sai wani jikan tsohon nan ya zo bayan shekaru 100 ya ce Adam Ashaka ya musu rashin mutunci, ya ci galba a kansu kuma ya yàƙe su bai musu adalci ba. Laifin Adam Ashaka shi ne ya yi ɗawainiya ya musuluntar da kakansu. Shi ma Shehu Ɗanfodiyo laifinsa ɗaya shi ne ya hana kakanninsu bautar gunki da dodo da tsumburbura.

Ƙarshen lalacewa shi ne ka ce za ka samo tarihinka wajen maƙiyinka bature, kun yarda malamai su ba ku ilimin sallah da zakka amma ba ku yarda da su ba a kan tarihin addininku da na Ɗanfodiyo ba, akwai hàukar da ta wuce wannan?

Shehu ai kafin Allah ne, ba abin da na ɗauki wannan abin face kawai Allah ne yake son ambaton Shehu ya ci gaba da wanzuwa sai ya ƙaddaro wannan abin. A soke shi ya samu lada sannan bayin Allah na ƙwarai su yi ta masa addu'a suna karanta littattafansa yana ƙara samun lada a kan lada. Wannan shi ne. ❤️

Allah saka wa Shehu da alheri, shi ma Adam Ashaka Allah biya su da aljanna da iyayenmu.

04/23/2026

⚠️ ABUBUWA 5 DA YA KAMATA KA KULA DASU A RAYUWARKA…

1️⃣ Addininka
Domin shi ne zai ceci ka a ranar da babu wani taimako.

2️⃣ Lokacinka
Domin duk ranar da ta wuce, ba zata dawo ba.

3️⃣ Zuciyarka
Kada ka bari zunubi ya kashe ta har ka daina jin tsoron Allah.

4️⃣ Abokanka
Domin su ne zasu iya gina ka ko su lalata ka.

5️⃣ Ayyukanka
Domin su ne hujjar ka a gaban Allah.

Ka gyara wadannan guda 5,
rayuwarka zata fara canzawa.

Want your business to be the top-listed Beauty Salon in Memphis?
Click here to claim your Sponsored Listing.

Telephone

Website

Address

Memphis, TN