MWALA

MWALA

Share

Contact information, map and directions, contact form, opening hours, services, ratings, photos, videos and announcements from MWALA, Health/Beauty, Abuja.

16/09/2026
03/09/2026

Abu biyu masu ban tsoro akan makomar arewa;
----------------------------

1. Da tsakar rana na haɗu da wata matar aure, ta goyo yaro a bayan ta, da wasu yara guda biyu riƙe a dama da hagun ta

Zafin rana na dukan jikin matar, yaron dake goye a bayan ta sai kuka yakeyi, takalmin matar ya tsinke 🥹💔

Nace; Mama ina zuwa haka? Tace ɓarayi sun bada sanarwar shigowa, shine muka gudu zuwa cikin gari

Nace; Kina da 'yan uwa acikin gari ne? Tace a'a zata nemi guri ta ɓuya a gidan mai ko makaranta 🥹💔

= Wallahi sai da hawaye ya zubo a ido na.

Akwai irin wannan matar sunfi dubu hamsin dake gudun hijira da ƙananan yara a arewa, saboda matsalar tsaro.

Sauro, iskan damina, zafin rana, ruwan sama duk a kansu yake ƙarewa.
----------------------------

2. Wani abokina dake kasuwanci a jahar Lagos yake gayamin;

Matan hausawa dake gudun hijira a Lagos, mafiyawansu amfani akeyi dasu (zina) ana biyansu kuɗi domin su samu abinda zasu siye abinci da magani 🥹💔

Yara mata masu shekaru 13,14,15,16 duk an lalata su da iyayensu saboda su 'yan gudun hijira ne

A t**i ƙarƙashin gada ake zina da yaran mu domin a basu abinci 😭🥲
----------------------------

⚠️ Ku cire kwaɗayi da neman duniya ku zaɓi shugaba nagari wanda zai kawo mana tsaro

Idan bahaka ba, billahillazi abunda yake faruwa a yanzu fiye dashi zai faru zuwa gaba

Wannan matsalar tsaron da kuke gani, sai ta mamaye ƙauye da birni idan mukayi wasa.

⚠️ Ku daina ɗaukar siyasa amatsayin hanyar neman kuɗi da arziki

Ka tambaye kanka, shin menene makomar 'ya'yan da zaka haifa zuwa gaba??

30/08/2026

2027: “Zan Sake Buɗe Iyakokin Ƙasa, In Gina Tashoshin Jiragen Ruwa a Kudu Idan Aka Zaɓe Ni” — Atiku

Ɗan takarar shugaban ƙasa na jam’iyyar ADC, Atiku Abubakar, ya yi alƙawarin cewa zai sake buɗe iyakokin Najeriya na ƙasa tare da bunƙasa tashoshin jiragen ruwa da ke kudancin ƙasar idan aka zaɓe shi a matsayin Shugaban Ƙasa.

Atiku ya ce matakan za su taimaka wajen ƙarfafa harkokin kasuwanci, ƙara samar da guraben ayyukan yi da bunƙasa tattalin arzikin Najeriya.

Want your business to be the top-listed Beauty Salon in Abuja?
Click here to claim your Sponsored Listing.

Category

Website

Address


Abuja

Alerts

Be the first to know and let us send you an email when MWALA posts news and promotions. Your email address will not be used for any other purpose, and you can unsubscribe at any time.

Subscribe

We will notify you when anything happens in Abuja.