SS GLISTEN
We offer solutions to your skin & hair problems.
14/09/2025
1. Yanayin Fatar Jiki (Skin Type)
-Idan kinada oily skin lotion zaiyi wahalar shiga fatar ki, saboda yanayin maikon fatar. Dole ne ki yi amfani da lotion da yake type na fatarki, ko Kuma Wanda yake for all skin types.
-Idan fata ƙaƙƙarfafa ce (thick skin) ko kuma irin mai bushewa sosai, lotion zai iya kasa shiga cikin zurfin fatar.
2. Matsalar Exfoliation,
rashin cire ƙwayoyin fata matattu (dead skin cells) akai-akai, yana hana lotion shiga fatar jiki sosai. Yana tsayawa ne saman fata. Dole sai kin nemi scrub kina amfani dashi a kalla kiyi exfoliating fatar jikin ki, cikin sati sau 1-2.
3. Yanayin Lotion ɗin da k**e amfani dashi.
Wasu lotions suna da formulation mara kyau (ba su da isassun humectants kamar glycerin, hyaluronic acid ko emollients kamar shea butter).
Idan lotion ya ƙunshi sinadaran da basu dace da fatar ki ba, zai hana yayi miki aiki yadda ya kamata.
4. Yanayin Wurin da ake zaune (muhalli)
-Iska mai sanyi ko bushewa (dry climate) na iya hana lotion aiki sosai saboda danshin fata yana bacewa da sauri.
-Yawan zama a wurin AC ga wasu, ko amfani da sabulu mai ƙarfi yana iya busar da fata fiye da yadda lotion zai iya gyarawa.
5. Yanayin yadda k**e Shafa lotion.
-Ki rika shafa lotion nan da nan bayan kin fito wanka, lokacin da fata take da ɗan ɗumi da danshi, domin hakan yana taimakawa sosai lotion ya shiga cikin fata yadda akeso.
-Haka kuka ki Kula da yadda k**e shafawa kowace gaba da Kuma yadda k**e murza lotion din ga fatar jiki. Ba wai ki rika tsakurowa Dan kadan ba, ki murza ga hannu buzubuzu ki shafe fuska da jiki Zui daya ba.
6. Matsaloli na rashin Lafiya. Ko matsalolin fatar jiki kamar eczema, psoriasis ko ichthyosis, lotion zaiyi matukar wahalar karbar fatar jiki. Dole sai kin fara magance wannan matsalar.
30/08/2025
1. Bushewar fatar kai. Idan fata ta bushe, tana iya yin ƙura-ƙura ta zube kamar farin ƙwaya.
2. Yawan mai a fatar kai (seborrheic dermatitis) Wannan cuta ce da ke sa fatar kai ta yi ja, ta kumbura, sannan ta fitar da farin ƙwayoyi cutar masu mai.
3. Ƙwayar fungus (Malassezia): ƙwayar fungus da ke rayuwa a fatar kai tana iya yawaita ta sa ƙaiƙayi da dandruff ya fara fitowa.
4. Rashin tsafta da wanke gashi akai-akai: Idan ba a wanke gashi ba, mai da ƙura suna taruwa sai su kawo dandruff.
5. Amfani da sinadarai masu ƙarfi kamar Relaxer, gel, da wasu shampoo dake dauke da sinadarai masu karfi suna iya fusata fatar kai daga karshe sai dandruff.
6. Rashin daidaiton hormones: Sauyin hormones (misali a lokacin balaga ko ciki) na iya kawo dandruff.
7. Abinci mara kyau. Rashin vitamin B, zinc, da omega-3 fatty acids yana iya shafar lafiyar fata da kai.
8. Tashin hankali/ damuwa/ gajiya (stress) Yana ƙara tsananta matsalar dandruff.
9. Yanayi lokacin sanyi da iska, ana samun bushewar kai, hakan yana iya sa dandruff ya ƙaru.
10. Cututtuka: Wasu matsalolin fata kamar eczema da psoriasis suna iya haifar da dandruff.
13/08/2025
Wasu amfanin turaren gashi (hair perfume/ hair mist) guda 6 masu muhimmanci ga lafiyar gashinkai da fatar kai. 👇🏼
1.Turaren gashi, yanada Ƙamshi mai daɗi.Yana kawar da duk wani bashi-bashin hamamin gashi, ya sanya lallausan ƙamshi, mai laushi wanda zai iya ɗaukar lokaci ko yini gaba ɗaya.
2. Wasu hair perfumes suna ƙunshe da sinadarai masu yin protective layer don hana wari shiga cikin gashi.
3. Turaren gashi (hair perfume) yana Ƙara laushi da sheƙi bawai iya kar kamshi ne amfani sa wajenki ba.Yawancin turaren gashi (musamman na SS GLISTEN ) yanada da light oils da silk proteins da ke sa gashi ya yi laushi da kyalli.
4. Yana kara danshin gashi, musamman Wanda baa hadashi da alcohol ba, musamman lokacin hunturu.
5. Turaren gashi yana taimakawa sosai wurin kare launin gashi ki. Saboda yana ɗauke da UV filters da ke kare launin gashi.
6. Yana karfafa fatar kai, sbd yana da essential oils kamar lavender, rosemary, ko peppermint, yana Kuma taimakawa sosai wajen motsa jinin kai da rage ƙaiƙayi.
07/08/2025
1. Sirrin Kula da Kanki (Self-care secrets)
-Ya kunshi, yawaita tsafta,yin wanka akai-akai, musamman a lokacin zafi da lokacin da k**e al'ada.
-Shafa mayuka masu kyau (misali irin na kamfanin ss glisten) bayan wanka. Wannan yana taimakama fata ta kasance cikin laushi da ƙyalli Koda yaushe.
-Idan kinada aure ki samu turaren wanka masu kyau kina zubawa cikin ruwan wankanki, ki lizimci amfani da kamshi ta ko ina,lungu, da sako, ki zaɓi kamshi mai laushi da ke nuna tsafta da sanyaya zuciya.
-Ki tsaftace gashinki, ki rika gyaran gashinki ado mai kyau, ki kamsashe gashinki, ki yi kitso mai kyau, ta ko ina dai gashin kanki ya zamo da tsabta.
2. Sirrin Hankali da Natsuwa (Mental and emotional beauty)
-Ki samu littafan ilimi na sanin duniyarki da lahirarki kina Karantawa. Wannan zai ƙara miki fahimta da basira cikin rayuwarki.
-Ki guji hayaniya da gulma, Natsuwa da kamun kai na kara daraja ga mace.
-Ki iya yin shiru lokacin da ya dace, hakan na nuna hikima da haiba.
3. Idan kina da aure kiyi kokari kisan sirrin Soyayya da zaman aure.
-Ki kula da yanayin maganarki, ki kula da kalmomin da k**e furtawa Koda yaushe, kada ki zazzaga baki ko zagi.
-Ki rika sauraro da fahimtar mijinki, saboda Sauraro da fahimta na gina zaman lafiya.
-Ki rike sirrin gidan aurenki, Kada ki rika bayyana sirrin aurenki.
4. Kisan sirrin Shiga na suturar dake karbar jikinki.
-Ki rika saka kaya masu tsafta da dacewa da halinki, ba dole su zama masu tsada ba.
-Ki guji ado mai yawa wanda ya saba ma sharia da kuma al'adarki.
-Kula da sutura da take kare mutuncinki.
5. Kisan sirrika na kula da lafiyarki da Kuma Kyawon Fatarki.
-Shan ruwa sosai, yana gyara fata da sosai.
-Cin abinci mai gina jiki kamar fruits, vegetables, protein.
-Ki guji yawan amfani mayuka masu haɗari ga jiki (bleaching creams, etc).
-Shan lemon tsami da zuma da safe yana taimakawa wajen tsaftace ciki da fata.(Ga wayanda Keda lafiyar Shan lemun tsami)
6. Ki rike sirrin Ibadah, ki cika zuciyarki da Imani, da Kuma yarda da Ubangiji.
-Ki yawaita addu’a da istighfari, yana samar da natsuwar zuciya.
-Yawaita godiya ga Ubangiji yana ƙara haske da kwanciyar hankali ga zuciya.
-Sallah da yawaita nafiloli kyakkyawar niyya, suna d
05/08/2025
Wasu daga cikin hanyoyin da zasu iya taimakawa wurin ƙara tsawon gashi cikin sauri da Kuma lafiya:
1. Amfani da mayukan dake dauke da ingantattun oils kamar misalin:
Man kwakwa (Coconut oil) yana cike da sinadarin lauric acid wanda ke shiga sosai kasan zurfin gashi ya karfafa shi.
Man zaitun (Olive oil) yana hana karyewar gashi da taimakawa wajen girma.
Man castor (Castor oil) yana dauke da ricinoleic acid, wanda ke kara jini a fatar kai, yana kuma kara tsawon gashi sosai da sosai
2. Cin Abinci Mai kyau da ina Jiki misali👇🏼
Protein: Gashi yana bukatar sinadarin protein domin gina kansa. Cin kifi, kwai, nama da wake yana taimaka wa gashi tsawo da yawa.
Iron, Zinc da Biotin (Vitamin B7): suna taimaka wa wajen gina gashi da hanashi zubewa.
Vitamin C da E: suna kare gashi daga lalacewa da kuma sa shi ya yi lafiya da tsawo.
3. Yin Massage na Fatar Kai.Yin tausa (massage) a fatar kai yana kara sa gudanar jini/ yaduwar jini wanda ke taimaka wa asalin gashi girma da sauri. Kina iya yin kamar mintuna 5–10 ana Miki tausar a rana da yatsun hannu ko brush.
4. Ki guji yawan amfani da heat tools kamar straightener, dryer, da curler.
5. Ki rage yawan tsuke gashi da karfi (tight hairstyles).
6. Ki rika amfani da comb mai hakora masu da tsakani don kada gashi ya karye.
7. Idan zakiyi amfani da Shampoo da Conditioner kiyi amfani da shampoo marar sinadarin sulfate da conditioner mai moisture domin kare gashi daga bushewa da karyewa.
8. Kada ki wanke gashi fiye da sau 2 ko 3 cikin sati.
9. Kina iya yin mask da hadin Aloe vera da man kwakwa, Suna kara danshi da kuma karfafa asalin gashi.
10. Ganyen hibiscus, curry leaves, ko fenugreek (hulba) suna saurin saka gashi tsawo idan ana amfani dasu matsayin mask.
11. Samun bacci isasshe da hutu yana rage wata damuwa, wanda hakan zai taimaka wurin Hana zubewar gashi ta dalilin damuwa.
12. Shan Ruwa yana taimakawa wajen Kara samun danshin gashi daga cikin jiki.
13. Ki gwada amfani da magic hair booster na ss glisten, yana kunshi da sinadarai da suke inganta lafiyar gashi, da Kara tsawon gashi, yawa da Kuma baki.
04/08/2025
Hanyoyin da ya kamata ku rika bi wurin kula da fuska Koda yaushe👇🏼
1. Wanke fuska sau biyu a rana.
2. Idan kina amfani da da toner, to ki rika amfani da wacce batada Alcohol
3. Ki dinga kokari kina moisturizing fuskarki
4. Kada ki taɓa tsallake SPF da safe.(ki dinga amfani da sunscreen a Koda yaushe domin kare fatar ki daga hasken rana daka iya cutar da fata, so samu ki rage shiga rana)
5. Exfoliate a kalla ko sau 1zuwa 2 ne, cikin sati. Ki Kula ba fa kullum kowane lokaci zakiyita scrubbing fatar ki ba toh.
6. Wannan kwalliya da k**e cika fuska dashi, ki dan dinga barin fata tana samun hutu, kada ya kasance kullum cikin make up, cikin shafa mai wannan yana toshe kofofin (pores) ta yanda fata ba zata iya fitar da maikon jikin ta ba, yana komawa kasan fata ya dankare wanda hakan ke haifar da kuraje.
7. Ko da yaushe ki rika dubin abinda ke miki aiki, sai ki tsaya gareshi. (baason canje-canje mayuka sosai).
02/08/2025
Gyaran fatar jiki da ta bushe (dry skin) yana buƙatar kulawa ta musamman domin dawo da damshi- damshin fatar jiki, da Kuma laushi.
Ga kadan daga matakan da zaku iya bi dan magance matsalar.
1. Amfani da sabulai marar sinadarin sulphate (mild soap).
2. Amfani da sabulai masu aloe vera, shea butter, ko oatmeal suna taimakawa sosai.
3. Wanka da Ruwa masu ɗumi ba masu zafi ba.
4. Idan an fito wanka ayi saurin shafa Mai da dan sauran danshin ruwan jikin.
5. Mayukan da za'a shafa su kasance moisturizers ne da ke kunshe da ceramides, glycerin. Haka Kuma za'a iya amfani da shea butter, coconut oil, olive oil, petroleum jelly.
6. Yawaita shafa Moisturizer akai-akai
6. Ku guji duk wani abubuwan da ke ƙara busar da fata
7. Dole ne ku guji sabulai ko mayuka na bleaching. Da duk wani sinadarai masu ƙarfi a jiki.
8. Rage yawan amfani da soso (sponge) mai kaifi.
9. Shan ruwa da Kuma isasshen abinci
10. Cin abinci mai omega-3, (kifi, gyada, avocado), vitamin E da C, suna taimakawa ga lafiyar fata.
11. Amfani da sunscreen ko yawaita saka hijabi don Kare fatar jiki daga rana.
01/08/2025
Dalilan dake sa bushewar fatar jiki sunada da yawa, daga ciki akwai yanayin muhalli da Kuma yanayin jiki.
Ga Kuma Karin kadan daga cikin wasu dalilan:👇
1. Karancin danshi ga Jiki:
Shan ruwa kadan yana hana jiki samun isasshen danshi daga ciki.
2. Sanyi ko iska mai karfi:
Yanayin sanyi ko iska mai ƙarfi nasa danshin fatar jiki ya bushe
3. Wanka da sabulai masu karfi.
Yawan amfani da sabulai masu sinadarai masu ƙarfi (kamar alkaline soaps) na iya cire natural oil ga fata.
4. Wanka da ruwa masu zafi sosai.
Yawan wanka da ruwan zafi na kashe natural oil da ke hana fatar jiki bushewa.
5. Matsala rashin lafiya (wani cuta a jiki, misali irin eczema, psoriasis, da Kuma diabetes) na iya haddasa bushewar fata.
6. Tsufa (Aging):
Shekaru idan sun fara tafiya, Kuma babu kulawa sosai, yana kawo bushewar fatar jiki saboda raguwar sinadaran dake kare fata.
7. Zafin rana (Sun exposure):
Yawan shiga zafin rana yana sa fatar jiki ta bushe.
8. Mayukan shafi masu karfi suna kawo bushewar fatar jiki, shiyasa yanada kyau idan zakiyi amfani da Mai ki fara sanin yanayin fatar jikin kafin ki
ga shafa Mai.
14/07/2025
Yadda zaaku gyara fuskar da ke fama da matsalar kurajen pimples:
1. Tsabtace Fuska akai-akai.
Wanke fuska sau 2 a rana (safe da dare) da sabulu Wanda bayada sinadarai masu ƙarfi (misali sulfate-free soap)
2. Ku guji amfani da sabulai ko bleaching creams
3. Za a iya amfani da waɗannan:
-Salicylic acid (2%): Yana taimakawa wajen buɗe kusurwar fata da rage kumburi.
-Benzoyl peroxide (2.5–5%): Yana kashe kwayar cutar da ke haifar da kuraje.
-Niacinamide: Yana rage redness da inflammation.
-Azelaic acid: Yana rage hyperpigmentation da sauya launin fata bayan kuraje.
Kada a cakuda chemicals da yawa lokaci guda ku zaɓi ɗaya ko biyu ku gwada kuyi amfani dashi kamar sati 2 zuwa 1month.
4. Kula da shinfidar gado dole ne sukasance tsaf tsaf Koda yaushe.
5. Ku rage yawan taba fuska da hannu mara tsafta.
6. Ku daina yawan cika fuska da kayan kwalliya masu nauyi (heavy makeup).
7. Yawaita shan ruwa sosai, A kalla ruwa lita 2 a rana yana taimakawa
8. Kula da abinci da kuke ci: Rage mai, madara, sugar, da fried foods.
9. Steaming fuska sau 1 cikin sati yana taimakawa bude duk wani kusurwar fatar fuska.
10. Kuna iya amfani da Tea Tree Oil: A shafa da ruwa sosai saboda yana da ƙarfi.
11. Aloe vera: Yana rage kumburi da kuma taimakawa wajen warkar da fata.
12. Amfani da Products masu inganci (misali SS GLISTEN products) yana taimakawa sosai wurin gusar da wannan matsalar pimples sosai.
13. Idan matsalar yayi yawa anyi duk wani dabaru da magani beyi ba. Ku ziyarci likitan fata (dermatologist).
SS GLISTEN
07/07/2025
📌
Click here to claim your Sponsored Listing.
Category
Contact the business
Telephone
Website
Address
Birnin-Kebbi
.
Opening Hours
| Monday | 08:00 - 18:00 |
| Tuesday | 08:00 - 18:00 |
| Wednesday | 08:00 - 18:00 |
| Thursday | 08:00 - 06:00 |
| Friday | 08:00 - 06:00 |
| Saturday | 08:00 - 06:00 |
| Sunday | 08:00 - 06:00 |
