Othman Muhammad Othman

Othman Muhammad Othman

Share

Assalamu alaikum my is Babangida from gombe

21/10/2023

SHAKAKIN MAZA DAN SHEHU KUNUN GABARUWA CIKA CIKI KAS MAKOGWARO:πŸ˜πŸ‘‘πŸ”₯

Allah Ya Kara Shiga Tsakanin Nagari Da Mugu, Allah Ya Kara Shiga Cikin Dukkan Lamuran Sarki, Allah Ya Karawa Sarki Kwazo Da Himma Cikin Aikin Mulkinsa..πŸ™πŸ‘βœŠπŸ€²πŸ”₯πŸ‘‘πŸ˜

13/10/2023

A KIYAYI SARKI A KIYAYI DODO:πŸ˜πŸ‘‘πŸ”₯

Allah Ya Kara Dafawa Sarki Cikin Dukkan Lamuransa, Allah Yasa Lahiran Sarki Tafinan, Allah Yasa Sarki Ya Gama Da Duniya Lafiya.πŸ€²βœŠπŸ‘πŸ™πŸ‘‘πŸ”₯🐘

05/10/2023

GARBA SADAUKI GARBA GAGARE GARBA RUWAN DARE DAMA DUNIYA:🦁πŸ”₯πŸ‘‘

Allah Ya Kara Tsole Idanun Maqiyan Sarki, Allah Duk Wanda Ya Damu Sarki Allah Ya Dameshi, Allah Ya Karawa Sarki Lafiya Da Kwanciyan Hankali.πŸ™πŸ‘βœŠπŸ€²πŸ”₯πŸ‘‘πŸ¦

04/10/2023

BISMILLAHIR RAHMANIR RAHEEM

HATSARIN MUTUWA DA BASHI AKAN KA

Manzon Allah (S.A.W) Yace: β€œNa Rantse Da Wanda Raina Yake Hannunsa, Da Za'a Kashe Mutum Ta Hanyar Ɗaukaka Addinin Allah (ο·»), Sai A Rayar Dashi, Sannan A Sake Kashe Shi, Sannan a Ƙara Rayashi, Sannan a Sake Kashe Shi, Sannan a Kuma Kashe Shi Da BΓƒSHI Akansa, Bazai TaΙ“a Shiga Aljannah ba Har Sai An Biya Masa Wannan Bashin”.
{NisΓ£'i Ya Ruwaitoshi}

Allah ya tsare mu. Allah yasa mudace duniya da lahira Bijahi Rasulillahi (S.A.W)

26/09/2023

BISMILLAHIR RAHMANIR RAHEEM

KUNJI MANZON ALLAH SALLALLAHU ALAIHI WASALLAM

Bayan an kammala yaqin Hunainu, yayin da Manzon Allah (S.A.W) yazo rabon kayan ganimah, sai ya rarrabata atsakanin mutanen Makkah da sauran Qabilun larabawa wadanda basu dade da shiga musulunci ba.

Mutanen Madeenah kuwa (AL ANSAR) bai basu komai ba. don haka sai wasu daga cikinsu suke mamakin mai yasa Manzon Allah (S.A.W) bai raba ganima dasu ba? Alhali tare dasu akayi gwagwarmayar nan!!

Da maganar tazo kunnensa (S.A.W) sai ya tarasu gaba dayansu waje guda yayi musu jawabi mai ratsa zukata, sannan daga karshe yace musu :

"SHIN YANZU BA ZAKUYI FARIN CIKI BA, SAURAN MUTANE ZASU KOMA GUDAJENSU DA AWAKI DA TUMAKAI DA ZINARE DA AZURFA, KU KUMA ZAKU KOMA GIDANKU TARE DA MANZON ALLAH!!!".

Sai s**a fashe da kuka suna cewa "Munyi farin ciki mun yarda da Manzon Allah (S.A.W) Shine rabonmu, shine kasonmu!!".

Allah yi salati da amincinka mafi girma bisa Annabinka mafi daraja, Shugaban mutanen farko dana karshe, mai tutar godiya aranar tsaiwa, Annabinmu Muhammadu tare da iyalan gidansa masu daraja da Sahabbansa madaukaka da dukkan mabiya bayansu da kyautatawa har zuwa ranar sakamako.

Amin Ya Hayyu Ya Qayyum πŸ™

24/09/2023

BISMILLAHIR RAHMANIR RAHEEM

NASIHA CE:

Ganin Girman Zunubi

Al-Hasan Al-Basriy _rahimahullah_ ya ce: Mutum yakan yi wani zunubi da zai kasa mantawa, yana ta jin tsoron wannan zunubin yana damuwa a zuciyarsa har sai wannan zunubin ya shigar da shi aljanna (Saboda girman da-na-sanin sa). KitΓ buz Zuhd na Imam Ahmad 1604.

Ibnul Qayyim _rahimahullah_ ya ce: "Idan Allah yana son alheri ga mutum sai ya cire masa ganin alhairansa daga zuciyarsa b***e kuma ya furta su da harshensa. A maimakon haka sai ya yi ta nuna masa zunubansa ya rika kallon su (yana da-na-sani har su shigar da aljanna) Dariq Al-Hijrtain, na Ibn A-Qayyim, shafi na 310.

Allah Yasa Mudace Duniya Da Lahira Bijahi Rasulillahi (S.A.W).

10/09/2023

BISMILLAHIR RAHMANIR RAHEEM

Ya Allah Ka jikan iyayen mu.
Ka albarkaci rayuwar mu.
Ka sauΖ™aΖ™a mana al-amuran mu.
Ka yaye mana bakin ciki.
Ka karemu daga dukkan sharri.
Ka hanemu aikata zunubi.
Ka cire mana hassada da girman kai.
Ka iya mana abinda ba zamu iya ba.
Alfarmar fiyayyen halitta (S.A.W).

Ina Muku Fatan Alheri Da Kuma Barka Da Safiya.

06/09/2023

BISMILLAHIR RAHMANIR RAHEEM

MAGANA DAGA QABARI

Yazo acikin littafin Ahwalul Qubur na Ibnu Rajab cewa Manzon Allah (S.A.W) yace :

"Duk lokacin da aka zo sanya mamaci acikin Qabarinsa, Qabarin zai yi kiransa yace :

"KAICONKA YA KAI DAN ADAM!!! WANENE YA RU'DAR DAKAI GAME DANI NE?

"SHIN BAKA SAN CEWA NINE GIDAN FITINA BANE!! KUMA GIDAN DUHU, KUMA GIDAN KA'DAITAKA, KUMA GIDAN TSUTSOTSI!!".

Ya Allah ka sanya Qaburburanmu su zamto dausayoyin Aljannah, ka yalwata mana makwantanmu, Ka haskaka mana cikinsa, Ka kiyaye mana jikkunanmu daga tsutsa kamar yadda ka kiyaye zukatanmu daga shirka alokacin da muke raye.

Ya Allah ka sanya hasken fuskar Annabinka ya zamto abin debe kewarmu daga kowanne razani da tashin hankali, ka sanyamu cikin wadanda taimakonka ke tare dasu aduniya da lahira.

Amin Ya Hayyu Ya Qayyum.

03/09/2023

Babu Wani Arziki Daya Kai Ka Wayi Gari Kana Musulmi Zuciyarka Cike Da Soyayyar Manzon Allah ο·ΊπŸ€—β€οΈ

31/08/2023

BISMILLAHIR RAHMANIR RAHEEM πŸ™πŸ™πŸ™

NASIHA CE:

HANYAN TSIRA DAGA WUTA ZUWA ALJANNAH:

Sahl dan Abdallah yace hanyan tsira uku ne:

Na farko shine cin halal
Na biyu aikata duk abinda yake wajibine akanka (Farilla)
Na uku koyi da Manzon Allah (S.A.W)

Duk wanda lizimce wannan abubuwa ukun tabbas yarabauta duniya da lahira.

Allah Yasa Mudace Duniya Da Lahira Bijahi Rasulillahi (S.A.W)

Ina Muku Fatan Alheri Da Kuma Barka Da Safiya.πŸ™πŸ™πŸ™

Want your business to be the top-listed Beauty Salon in Gombe?
Click here to claim your Sponsored Listing.

Category

Telephone

Website

Address


Gombe
BABBANYARO