ABU Sultan PKM
Contact information, map and directions, contact form, opening hours, services, ratings, photos, videos and announcements from ABU Sultan PKM, Health/Beauty, Tsohuwar Kasuwa Old Prison Raod Potiskum, Potiskum.
01/01/2026
JIBWIS YOBE STATE
Lafiya da zaman lafiya sune ginshikokin jin dadin rayuwa
Shugaban Jibwis na Jihar Yobe
Sheikh Imam Yusuf Adam Muhammad Damaturu
Ya yi kira ga dukkan 'ya 'yan kungiyar Izalah reshen Jihar Yobe baki ɗaya, akan su ƙara cigaba da Addu'o'i, Istigfari, sadaka, taimakon Al'umma da yin Alqunutu a masallatan kungiyar domin neman Allah ya bamu zaman lafiya a Jihar da ma ƙasa baki ɗaya.
Lalle muna Godiya ga Allah ya bawa jihar mu kariya da zaman lafiya, to mu ƙara cigaba da Addu'o'i ka'in da na'in sannan kuma 'yan Agajin mu su kara tsaurara tsaro a dukkan masallatan mu na Juma'ah da na Khamsul Salawat da sauran wuraren Ibada da Tarurruka.
Lalle a kula da dukkan shige da fice na Al'umma da Ababan hawa da kuma sa ido akan dukkan abinda ba'a amince da shi ba tare bada haɗin kai ga jami'an tsaro da iyayen ƙasa domin samun nasara.
Allah ya bamu zaman lafiya, Allah ya tsare mu daga dukkan sharrin masu Sharri da makirai da munafukai.
Jibwis Yobe State
Jibwis Social media Yobe State Directorate
12 Rajab, 1447
1 January, 2026
31/12/2025
SHIN HISBAR POTISKUM DIVISION BA'A BASU DAMAR AIKIN BANE KO DAI BAZASU IYA BANE......?
Wai shin ina HISBAR Potiskum ta shiga, kodai an haramta aiyukan tane?
Tabbas akwai bukatar ayi mata garanbawul don mu fara ganin aiyukan ta a kasa. Allah Ya musu jagora ameen
KWADAYI MA BUDIN WULAKANCI
Ka dena saurin karɓar kayan kowanne irin mutum da sunan kyauta ko sadaka a wannan zamanin da muke ciki. Wata kyautar tarko ce wadda aka ɗana maka kuma wallahi baka isa ka kufce ba matuƙar tarkon ya k**a ka a daidai. Akwai mutumin da pure water kaɗai zai baka, amma da duniya zata taru sai ya tabbatar musu cewa shine wanda yake shayar da kai ko mutuwa zaka yi bazai dena faɗa ba.
Wannan fa bawai sai abokan za Jiman ka ba, hatta a cikin gidan ku ma yana da kyau kasan inda dare ya maka. Not every kindness is a treasure. Ko a majalisar ku ake yawan kawo abinci ko wani abu mak**ancin sa, ya sheikh ka daure ka danne ƙwaɗayin ka saboda gudun wulaƙanci. A nan ba ina nufin ka dena ci ko kuma ƙarbar alheri ba ne, kawai dai kasan inda dare yayi maka ne. Kodai ka ɗauka, ko kuma ka watsar da abinda na faɗa maka. Amma tabbas za'a zo ranar da za'a yi maka gorin da zai taka maka bakin faranti idan ka kasa gane me nake nufi.
Click here to claim your Sponsored Listing.
Category
Contact the business
Telephone
Website
Address
Tsohuwar Kasuwa Old Prison Raod Potiskum
Potiskum
Alerts
Be the first to know and let us send you an email when ABU Sultan PKM posts news and promotions. Your email address will not be used for any other purpose, and you can unsubscribe at any time.
